Ana tuhumar shugaban Bayern Munich

Uli Hoenness Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Tsohon dan kwallon Jamus da Bayern Munich

Ana tuhumar shugaban kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich, Uli Hoeness, bisa zargin kin biyan haraji.

Masu shigar da kara na tuhumarsa da kauce wa biyan haraji da ya kai £2.9 miliyan.

Hoeness, tsohon dan kwallon Jamus dake cikin tawagar da suka lashe kofin duniya mai shekaru 62, ya amince da cewar yana da asusun ajiya na asirce a Switzerland.

Sai dai bai amince da yin kwaskwarimar kudin harajin da ya kamata ya biya a bara ba, da kin sanar da mahukunta dukiyar da ya mallaka.

Kaurace wa biyan haraji zai kai ga hukuncin daurin shekaru 10, masu shigar da kara sun ce za su bukaci hukuncin shekaru bakwai -- ana sa ran yanke hukunci ranar Alhamis.