Bikin wasan kofin duniya: ba jawabai

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Blatter na fatan wasan kofin duniyar zai sa mutanen Brazil su daina zanga zanga

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, ta ce ba za a yi jawabai a lokacin bikin bude gasar cin Kofin duniya da za yi a Brazil a watan Yuni ba.

A shekarar da ta wuce 'yan kallo sun yi wa shugabar Brazil, Dilma Rousseff, ihu, lokacin wasan farko na bude gasar cin kofin zakarun nahiyoyi, wanda share fage ne na wasan kofin duniyar.

A wata hira da manema labarai, Sepp Blatter, ya nuna damuwarsa kan tashin hankalin da ake yi a Brazil.

'yan kasar na tarzoma ne kan rashawa da yawan kudin da ake kashewa a shirin gasar kofin duniyar.

Karin bayani