Wasan Kofin Zakarun Turai

Image caption Bayern Munich ta yi waje da Arsenal a gasar Kofin Zakarun Turai

Kungiyar Bayern Munich ta Jamus ta kai wasan daf da na kusa da karshe bayan da suka tashi wasa da Arsenal ta Ingila daya da daya a gasar cin kofin zakarun Turai.

Tun a karawar farko da suka fafata a Emirates Bayern Munich ce ta doke Arsenal da ci 2-0.

Jumulla a karawa biyun Bayern Munich masu rike da Kofin Zakarun Turan na da ci 3 Arsenal kuma na da 1.

Itama Atlético Madrid ta Spaniya ta yi waje da AC milan ta Italiya, bayan da ta caskarata da ci 4 da daya.

Dan kwallon Atletico Madrid Diego Costa ne ya fara zura kwallo a minti na uku da na 85, Turan da Raúl García suka zura kwallo ta uku da ta hudu a minti na 40 da na 70.

Milan ta zura kwallon ta daya tilo ta hannun Kaká a minti na 27 ′, kuma wasan farko da suka kara a Italiya doke Milan aka yi da ci daya mai ban Haushi.

Jumulla wasa karawa biyu Atletico Madrid na da kwallaye 5 Milan na da 1.

Ranar Laraban nan za a ci gaba da wasannin na Zakarun Turai karo na biyu.

Barcelona za ta karbi bakuncin Man City, yayin da PSG za ta karbi Bayern Leverkusen.

A wasan farko Barca ta ci Man City 2-0, PSG kuwa ta ci Bayern 4-0.