Charlton ta kori kocinta Powell

Chris Powell
Image caption Kungiyar ta raba gari da Powell ne domin kar ta fice daga gasar Championship

Kungiyar Charlton ta raba gari da kocinta, Chris Powell, sakamakon tsintar kanta da ta yi a matsayi na karshe a gasar Championship. Kungiyar na shirin maye gurbinsa da Jose Riga.

Tun farko dai Powell, mai shekaru 44, ya nemi tsawaita kwantiraginsa da kungiyar, sai dai shugabanta Roland Duchatelet yaki amincewa bisa dalilai da dama da suka hada da rashin kokarin kungiyar a kakar bana.

Riga, mai shekaru 56, shi ne daraktan tsare tsare a makarantar horon 'yan kwallon AC Milan, kuma yana da kusanci da Duchatelet.

Charlton, wacce za ta kara da Huddersfield ranar Laraba, na bukatar maki hudu domin kaucewa fita daga gasar Championship.