FA ta dakatar da Pardew wasanni 7

Alan Pardew
Image caption Kocin ya nemi afuwar rashin da'ar da ya nuna

Hukumar kwallon kafar Ingila ta dakarar da kocin Newcastle Alan Pardew, wasanni bakwai sakamakon dukan David Meyler da ka.

Pardew, mai shekaru 52, sai da alkalin wasa ya kora shi cikin 'yan kallo bayan an dawo zagaye na biyu, a karawar da suka doke Hull da ci 4-1, a filin wasa na KC.

Kocin ya nemi afuwa bayan an tashi wasa, Newcastle ta ci tararsa £100,000 da kuma gargadinsa da ya guje wa sake faruwar haka a gaba.

Pardew, wanda ya fara kocin kungiyar a shekarar 2010, ba zai buga karawa da kungiyar za ta yi da Fulham da Crystal Palace da Everton da Southampton da Manchester United da Stoke City da kuma Swansea ba.