Dangote zai ba 'yan wasan Nigeria $1m

Alhaji Aliko Dangote
Bayanan hoto,

Attajirin nan Tony Elumelu ya yi alkawarin ba wa 'yan wasan $ 500,000

Attajirin dan kasuwan nan na Najeriya, Alhaji Aliko Dangote ya ce a shirye ya ke ya ba wa 'yan wansan Super Eagles dala miliyan daya da ya yi musu alkawari.

Dangote ya yi alkawarin ne a watan Fabrairun da ya gabata, biyo bayan nasarar lashe gasar cin kofin zakarun nahiyar Afrika a shekarar 2013 da kungiyar kwallon kafar kasar ta yi.

Ya shaida wa BBC cewa "Mun yi ta jiran jami'an gwamnatin Najeriya su zo su karbi kudin, amma babu wanda ya rubuto mana takarda game da batun."

"Za mu rubuta musu takarda, mu nemi lambobin asusun 'yan wasan kuma nan take za mu zuba musu kudi a asusun nasu." Inji Dangote.

Jinkirin da aka samu wajen cika alkawuran da wasu masu kudi suka yi ne, ya sa me tsaron gidan Super Eagles, Vincent Enyeama ya yi kira a gare su da su cika alkawarin.