Mesut Ozil zai yi jinyar makonni hudu

Mesut Ozil Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dan wasan zai yi jinyar wata guda

Raunin tsagewar tsoka da dan wasan Arsenal Mesut Ozil ya ji zai sa ya yi jinyar makwanni hudu.

Dan kwallon Jamus, mai shekaru 25, ya ji raunin ne a karawar da suka yi da Bayern Munich a kofin zakarun Turai ranar Talata.

Ozil, ba zai buga wasan hamayya da Tottenham ranar Lahadi ba, da kuma wasannin Chelsea da Swansea da Manchester City a gasar cin kofin Premier.

Sannan kila ba zai buga wasan kofin FA ba, wasan daf da na karshe da za su fafata da Wigan ranar 12 ga watan Aprilu.