Ana tuhumar Cantona da cin zarafi

Eric Cantona
Image caption Cantona ya yi kaurin suna wajen rashin hakuri

'Yan sanda sun tsare tsohon dan kwallon Manchester United Eric Cantona, bisa tuhumarsa da cin zarafi a Arewacin Landan.

Lamarin ya faru ne a Regent Park Road, a Camden ranar Laraba.

An garkame dan wasan daga baya ya sha tambayoyi daga jami'an tsaro, shi kuwa wanda aka ciwa zarafin bai bukaci taimakon gaggawa daga likitoci ba.

Cantona dan Faransa ya lashe kofunan Premier hudu tare da Manchester United, kafin ya yi ritaya ya koma wasan fina-finai.