Jerin kasashen da suka fi iya taka leda

Fifa Logo
Image caption Najeriya ta gusa sama zuwa matsayi na 7 daga mataki na 8

Masar da Guinea sun gusa sama a jerin kasashen da suka fi iya taka leda a duniya da Afirka na watan Maris da aka fitar ranar Alhamis.

Masar ta yi tashin gwauron zabi daga matsayi na biyar ta koma mataki na uku a Afika, kuma ita ce ta 26 a duniya; Guinea ta koma matsayi na tara daga matakinta na 11 a baya.

Masar ta doke Bosnia da Herzegovina 2-0 a wasan sada zumunci, Guinea ita kuma ta samu nasara akan Iran da ci 2-1, dalilan da ya sa suka gusa sama a jerin kasashen da suka fi iya taka leda a duniya da Afirka.

Najeriya ma ta gusa sama daga mataki na takwas zuwa matsayi na bakwai, bayan baga wasa babu ci da suka fafata da Mexico a Amurka.

Har yanzu Ivory Coast ce ke rike da matsayin ta daya a Afirka ta 24 a duniya.

Sauran kasashen da ke jerin goman farko sun hada da tsibirin Cape Verde da Ghana da Cameroon da Mali da suka dawo kasa da taki daya, Afirka ta kudu na matsayinta na 12 duk da doke ta da Brazil ta yi da ci 5-0 har gida

Ga Jerin kasahen da ke gaba wajen iya taka leda a Afirka da Duniya

1. Ivory Coast 24 2. Algeria 25 3. Egypt 26 4. Cape Verde 33 5. Ghana 35 6. Tunisia 44 7. Nigeria 47 8. Cameroon 50 9. Guinea 53 10. Mali 56