Afirka ta kudu na son daukar bakuncin kofin duniya

Banyana Banyana
Image caption Afirka ta Kudu na fatan daukar nauyin kofin Duniya ta mata 2019

Afirka ta kudu na shirin neman izinin karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta mata a shekarar 2019.

Tuni kasar ta samu izinin daukar bakuncin gasar cin duniya ta matasa 'yan kasa da shekaru 20, karon farko da za a gudanar da gasar a Nahiyar Afirka.

Afirka ta kudu za ta fuskanci kalubale daga mai rike da kofin duniyar Japan, wacce ita ma ke son karbar bakuncin gasar.

Shugaban hukumar kwallon kafar kasar, Danny Jordaan, ya ce tarihin karbar bakuncin gasar kofin duniya ta maza da sauran wasanni da suka yi ya kara musu kwarin gwiwa.

Jordaan ya ba da sanarwar daukar tsohuwar 'yar wasan Holland Vera Pauw, a matsayin sabuwar kocin Banyana Banyana.