Arsenal za ta ci tarar Bendtner

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nicklas Bendtner

Kungiyar Arsenal ta ci tarar Nicklas Bendtner saboda ya tafi Copenhagen ba tare da izini ba.

Sannan kuma kocinsa Arsene Wenger ya ce Bendtner din na kan hanyarsa ta barin Emirates.

Wenger yace "Yana cikin karshen yarjejeniyarsa kuma ba za a sabunta ba".

Bendtner ba ya cikin 'yan wasan Arsenal da suka kara da Bayern Munich a don haka sai ya tafi Copenhagen inda ya samu hatsaniya da wani direban tasi.

A yanzu haka dai Bendtner na fama rauni a idon sawunsa.

Karin bayani