Doiuf zai yi doguwar jinya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mame Biram Diouf

Dan kwallon Senegal Mame Biram Diouf zai yi jinya har karshen kakar wasa ta bana saboda ciwo a kafadarsa.

Diouf ya ji rauni ne lokacin wasan Hannover da Bayer Leverkusen a makon da ya gabata.

Diouf ya zura kwallaye 30 a wasanni 68 tun lokacin da ya koma Hannover a watan Junairun 2012.

Dan wasan mai shekaru 26 a karshen kakar wasa ta bana yarjejeniyarsa za ta kare a Hannover.