Nigeria ta soke wasanni a Maiduguri

Motar kulob din Elkanemi
Image caption An dakatar da dukkan zirga-zirgan jiragen sama zuwa birnin tun a shekarar da ta gabata

Gasar premier league ta Najeriya ta soke wasannin da aka shirya yi a birnin Maiduguri, saboda dalilai na tsaro.

Hakan ya biyo bayan rokon da kungiyar wasan Abia ta shigar, tana neman kada a yi karawar da aka shirya tsakaninta da El-Kanemi Warriors a filin wasa na Maiduguri a ranar Asabar.

Kungiyar ta Abia ta nuna fargabarta biyo bayan tashin hankalin da aka samu a birnin da kewayensa.

A wata sanarwar da ta fitar a ranar juma'a, gasar ta kamfanin Globacom ta ce "Saboda wasu dalilai da suka fi karfinmu, mun jingine dukkanin wasannin da aka shirya yi a Maiduguri har sai inda hali ya yi."