Na yi murnar doke Chelsea - Lambert

Paul Lambert
Image caption Kocin ya yaba da yadda yan wasansa suka doke Chelsea

Kocin Aston Villa Paul Lambert ya ce doke Chelsea 1-0, shi ne wasa mafi kayatar wa da kungiyar ta buga tun lokacin da ya zama kocin kulob din.

Dan wasan Vila Fabian Delph ne ya zura kwallo a raga bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Lambert ya ce ko kadan bai damu da aka kori 'yan wasan Chelsea William da Ramires da koci Jose Mourinho ba, kuma hakan bai kawo tsako da Villa ba.

Aston Villa ta koma cikin 'yan goman farko a teburin Premier, bayan data doke Chelsea a filin Villa Park ranar Asabar.