Doke Newcastle mun samu kwarin gwiwa

Felix Magarth Hakkin mallakar hoto empics
Image caption Kocin ya ce zai ci gaba da kokarin yadda za su zauna a gasar Premier

Kocin Fulham Felix Magath ya ce doke Newcastle 1-0 da suka yi, ya kara musu kwarin gwiwar ci gaba da neman zama a gasar Premier bana.

Ashkan Dejagah ne ya zura kwallo a raga, nasarar farko bayan wasanni 10 baya da suka buga, wacce kungiyar take neman maki hudu domin ci gaba da zama a gasar Premier.

"Na yi murna da muka doke Newcastle, kuma nasarar ta kara mana kwarin gwiwa" in ji Magarth wanda ya karbi kocin kungiyar a Fabrairu.

Nasarar da Fulham ta samu ita ce ta farko a wasanni hudu tun lokacin da Magath ya karbi ragamar Horar da kungiyar.