Liverpool ta doke Man United 3-0

Steven Gerrard
Image caption Gerrard ne ya zura kwallaye biyu a dukan fenariti

Kungiyar Liverpool ta doke Manchester United da ci 3-0 har gida, a gasar Premier wasan mako na 30 da suka kara a Old Trafford ranar Lahadi.

Steven Gerrard ne ya zura kwallaye biyu a dukan fenariti, bayan da Rafael ya taba kwallo da hannu da kuma Phil jones ya yi wa Joe Allen keta a da'ira ta 18.

Liverpool ta samu fenariti na uku bayan da Nemanja Vidic ya doki Daniel Sturridge aka kuma ba shi jan kati, sai dai Gerrard bai zura kwallon a raga ba, lokacin da ya buga kwallo ta doki turke.

Sai dai Luiz Suarez ya kara kwallo ta uku daf a tashi, hakan ya mai da Liverpool matsayi na biyu a teburin Premier da maki 62, United ta koma mataki na bakwai da maki 48.