Arsenal ta doke Tottenham da ci 1-0

Arsenal Win
Image caption Arsenal na matsayi na uku a teburin Premier da kwantan wasa daya

Kungiyar Arsenal ta doke Tottenham har gida da ci daya mai ban haushi a gasar Premier wasan mako na 30 da suka kara a filin wasa na White Hart Lane ranar Lahadi.

Rosicky ne ya zura kwallo a ragar Tottenham a minti na biyu da fara kwallo.

Tottenham ce ta mamaye wasa bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, kuma Adebayor ya samu damar farke kwallon da ya buga sai dai ta yi waje kafin a tafi hutu.

Nasarar da Arsenal ta samu ya sa tana matsayi na uku a teburin Premier da kwantan wasa daya, da tazarar maki hudu tsakaninta da Chelsea wacce Aston Villa ta doke ranar Asabar.