'Liverpool za ta iya lashe gasar Premier'

Image caption Gerrard ya ce za su bada mamaki

Kyaftin din Liverpool, Steven Gerrard ya ce kungiyar za ta iya lashe gasar Premier ta bana, bayan ta lallasa Manchester United da ci uku da nema a Old Trafford.

Gerrard ya zura kwallaye biyu a bugun fenariti kafin ya barar dana uku, sannan kuma Luis Suarez ya ci kwallo daya.

"Mun nuna cewar zamu iya lashe wannan gasar, kuma za a fafata damu har zuwa karshe," in ji Gerrard.

Rabon da Liverpool ta lashe gasar Premier ta Ingila tun a shekarar 1990, kuma a yanzu tazarar maki hudu ne tsakanin ta Chelsea wacce ke jan ragama.

Liverpool ta samu nasara a wasanninta takwas cikin 10 a wannan shekarar, kuma a cikin watan Afrilu za ta dauki bakuncin Manchester City da kuma Chelsea.

Karin bayani