Messi ya ci kwallaye uku

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Barcelona na kokarin rage tazara tsakaninta da Real

Lionel Messi ya haskaka a wasan da Barcelona ta lallasa Osasuna daci bakwai da nemi a gasar La Liga ta Spain.

Nasarar ta sa Barca ta rage tazarar makin dake tsakaninta da Real Madrid da kuma Atletico Madrid.

Dan kwallon Argentina din ya ci kwallaye uku, sannan Alexis Sanchez ya ci daya, a yayinda Iniesta da Tello da kuma Pedro suma suka ci kwallo daya-daya.

Sakamakon sauran wasannin:

*Elche 0 - 0 Real Betis*Sevilla 4 - 1 Real Valladolid*Real Sociedad 1 - 0 Valencia CF*Málaga 0 - 1 Real Madrid*Atlético Madrid 1 - 0 Espanyol*Levante 0 - 1 Celta de Vigo*Rayo Vallecano 3 - 1 Almería

Karin bayani