FIFA na shirin hukunta Anelka

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Anelka da abokinsa mai barkwanci Dieudonne M'bala M'bala

Hukumar kwallon kafa ta duniya-FIFA na tunanin dakatar da korarren dan wasan West Bromwich Albion, Nicolas Anelka daga harkar kwallon kafa a duniya.

Hukumar kwallon Ingila-FA ce ta bukaci FIFA ta dauki matakin bayan an same shi da laifin nuna kiyayya ga yahudawa.

FA ta dakatar da Anelka na wasanni biyar saboda nuna alamar da ya yi da hannunsa a watan Disamba.

Kakakin FIFA ya ce "Hukumar FA ta Ingila ce ta bukaci a dakatar da Anelka daga kwallo a duniya".

West Brom ta kori dan kwallon saboda ta sameshi da laifi, bayan ya bayyana raba gari da kungiyar a shafinsa na Twitter.

Karin bayani