Olle-Nicolle ne sabon kocin Benin

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Didier Olle-Nicolle

Jamhuriyar Benin ta nada dan Faransa Didier Olle-Nicolle a matsayin sabon kocin tawagar 'yan kwallonta.

Ya maye gurbin Manuel Amoros wanda ya raba gari da kasar.

Dan shekaru 52, Olle-Nicolle ya kulla yarjejeniyar da kasar har zuwa lokacin gasar cin kofin Afrika da za a buga a shekara mai zuwa.

A baya ya jagoranci kungiyoyin Valenciennes da kuma Nice.

Karin bayani