An zaftare kudin 'yan wasan Ghana

Masu yiwa 'yan wasan Ghana kirare Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Minsitan wasan Ghana, Elvis Afriyie Ankrah ya ce hukumomi na jiran martanin 'yan wasan game da batun

Tawagar 'yan wasan Ghana za su halarci gasar cin kofin duniya a Brazil aljihunsu ba nauyi, bayan an zaftare fiye da rabin kudaden da aka kasafta musu a baya.

Gwamnatin kasar ta ware $9 miliyan, da za ta baiwa 'yan wasan idan har sun kai ga zagayen karshe na gasar.

Amma ada ta shirya ba su $22 miliyan ne, amma ta zaftare bayan korafin da mutanen Ghana suka yi game da yawan kudin.

Ghana ta ware $19 miliyan ne a gasar cin kofin duniya da kasar ta halarta shekaru hudu da suka wuce.