'Drogba na cikin zaratan 'yan wasa'

Didier Drogba Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mourinho ya yi fatan komowar Drogba kulob din Chelsea

Manajan Chelsea Jose Mourinho ya yi amanna cewa, dan wasansu da ya kafa tarihi, Didier Drogba har yanzu yana cikin zaratan 'yan wasan gaba na duniya.

Didier dan wasan Galatasaray, wanda ya bar Stamford Bridge a watan Yuni shekarar 2012 ya dawo London, saboda zagaye na biyu na karawarsu a gasar zakarun Turai.

Mourinho ya ce "Yanzu a ce Drogba mai shekaru 36 daidai yake da lokacin da yake da shekaru 26? babu wanda zai zamo haka, amma babu tantama har yanzu yana cikin zaratan 'yan wasan gaba na duniya."

Drogba ya ce ba zai yi murna ba, idan ya zura kwallo a ragar kulob dinsa na da.

Dan wasan dan kasar Ivory Coast ya zura kwallaye 157 a wasanni 342 da ya yi a tsawon shekaru takwas da ya kwashe a Chelsea.