Robben na nan a Bayern har zuwa 2017

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Robben na cikin tawagar Bayern da ta lashe gasar zakarun Turai

Dan kwallo Bayern Munich Arjen Robben ya sabunta kwangilarsa don ci gaba da taka leda a kungiyar har zuwa shekara ta 2017.

Robben mai shekaru 30, ya koma Bayern ne daga Real Madrid a shekara ta 2009 a kan fan miliyan 24.

Tsohon dan wasan Chelsea din ya ce "Ina jin dadin taka leda a nan kuma iyalai ma sum gamsu".

Dan kasar Holland din ya zura kwallaye 10 a kakar wasa ta bana tare da Bayern.

Yana shirin lashe gasar Bundesliga a karo na uku a bana, kuma a baya ya lashe gasa a Ingila da Spain da kuma Netherlands.

Karin bayani