Schemelzer zai yi jinyar makonni 4

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Schemelzer dai ba zai samu buga zagayen quarter Finals na gasar ba.

Dan wasan baya na Borusia Dortmund Marcel Schmelzer ya shiga sahun 'yan wasan kungiyar da suka samu rauni.

Wata sanarwa da kungiyar ta fitar yau ta ce dan wasan zai kwashe makonni hudu bai shiga fili ba.

Dan wasan dan asalin kasar Jamus dai ya ci karo da kullewar jiyoji ne a cinyarsa yayin karawar da kungiyar tayi da Zenith St petersburg a jiya Laraba, wadda ta bai wa kungiyar damar wuce wa zuwa matakin quarter finals na gasar zakarrun Nahiyar Turai.

A yanzu dai Schelmezar shi ne dan wasa na biyar daga cikin 'yan wasan Borusia Dormund da suka tafi jinyar rauni a wannan zangon.

Karin bayani