Zakarun Turai: tsirar Man U da Dortmund

Image caption Manchester United ta tsallake rijiya da baya kasancewar a karawar farko an ci ta 2-0

A gasar kofin zakarun turai da aka fafata a Old Traford, Machester United takai wasan gab da na kusa da karshe bayan ta lallasa Olympiakos ta Girka da ci 3-0.

Robin Van Persie ne ya zura kwallaye 3 a ragar Olympiakos, a wancan karon da aka kafsa a Girka Olypiakos ta doke Man U da ci 2-0.

Hakan dai na nuni da cewar Manchester United ta yi galaba da ci 3-2 jumulla wato ta sami damar zuwa wasan gab da na kusa da karshe.

A cigaba da gasar Zenith Saint Petersburg ta bi Brussia Dortmund har gida inda ta doke ta da ci 2-1 sai dai hakarta ba ta cimma ruwa ba.

Domin a wancan karon Dortmund ta doke Zenith din da ci 3-2 wanda hakan ya sa Dortmund kasancewa zakara da ci 5-4, wato Dortmund ta sami damar zuwa wasan gab da na kusa da karshe a gasar.

A ranar Juma'a za afitar da yadda kungiyoyin da suka yi nasara zuwa matakin wasan gab da na kusa da karshen za su kara.

Karin bayani