UEFA: United za ta kara da Bayern

Kulob-kulob da suka tsallake a gasar Zakarun Turai Hakkin mallakar hoto bb
Image caption A watan Afrilu za a buga wasannin

Kulob din Manchester United zai fafata da Bayern Munich, a wasan na kusa da na kusa da na karshe a gasar Zakarun Turai.

Yayin da kulob din Chelsea zai kara da Paris St-German.

Kulob din Barcelona na Spaniya zai kece raini da Atlentico Madrid, sai Real Madrid da za ta kara da Borussia Dortmund.

Za a yi zagayen farko na wasannin ne a ranakun 1 da 2 ga watan Aprilu, yayin da zagaye na biyu kuma, za a taka ledar a ranakun 8 da 9 ga watan Aprilu mai zuwa.

Wasan karshe na gasar zakarun Turai za a yi shi ne, a ranar 24 ga watan Mayu, a filin wasan Benfica watau Estadio da Luz da ke Lisbon.