Kamaru:FIFA ta kara wa kwamitin riko wa'adi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kara wa'adin dai ya biyo ne bayan wata ziyara da wasu jami'an Fifa da CAF suka kai kasar a makon jiya.

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA ta kara tsawon wa'adin ikon da ta bai wa wani kwamitin daidaita lamurra da ta kafa domin gudanar da lamurran hukumar kwallon kafa ta kasar kamaru da wasu watannin takwas.

Wannan dai zai ba kwamitin rikon damar Jagorantar 'yan wasan Indomitable Lions zuwa Gasar Cin Kofin Duniya ta 2014 kuma ya ci gaba da aiki har zuwa ran 30 ga watan Nuwamba.

Hukumar ta FIFA ta kafa kwamitin ne ranar 22 ga watan Yulin bara da manufar bitar dokoki, da gudanar zabe da kuma tafiyar lamurran yau da kullum na hukumar ta FECAFOOT.

Kafa kwamitin dai ya zo ne bayan FIFA ta hana Kamaru shiga gasar wasannin da take shiryawa saboda yadda ta ce gwamnati ke tsoma baki cikin gudanar lamurran kwallon kafa a kasar.

Karin bayani