Shari'ar Pistorius za ta kai watan Mayu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shari'ar za ta shiga mako na hudu ne ranar Litinin.

Shari'ar kisan kan da ake yiwa dan tseren guragun nan na kasar Afrika ta Kudu Oscar Pistorius yanzu za ta gudana har zuwa tsakiyar watan Mayu; bayan bangarorin biyu sun amince su tsawaita shari'ar.

Tuni dai lokacin da aka kebe wa shari'ar ya kare ba tare da lauyoyi masu shigar da kara sun kammala gabatar da hujjojinsu ba.

Mr. Pistorius dai ya musanta bindige budurwarsa, Reeva Steenkamp da gangan, inda ya ce ya dauka wani ne ya shigo gidansa.

A makon jiya dai ya ce zai sayar da gidansa domin ci gaba biyan lauyoyin da ke ba shi kariya.

Karin bayani