Alkalin wasa ya roki Arsenal gafara

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A wannan wasan dai ne Chelsea ta lallasa Arsenal da ci 6-0.

Alkalin wasa Andre Marriner ya roki gafara kan korar dan wasan baya na Arsenal Kieran Gibbs da yayi bisa kuskure a wasan da Kulob din ya buga da Chelsea ranar Assabar.

An dai ba Chelsea bugun fenariti bayan da Alex Chambarlain ya taba kwallo da hannu a bakin gidan Arsenal, amma sai alkalin wasa ya nuna wa Gibbs katin kora.

Chambarlain dai yayi kokarin nuna wa Marriner cewa shi ne yayi laifin na taba kwallo da hannu, amma kuma alkalin wasan bai canza hukuncin ba.

A cikin wata sanarwa Marriner ya ce ya ji takaicin kuskuren da yayi na korar Gibbs.

Karin bayani