Arteta ya nemi afuwar masoyan Arsenal

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mikel Arteta

Dan wasan tsakiya na kulob din Arsenal Mikel Arteta ya nemi afuwa kan yadda suka buga wasa da Chelsea ranar Assabar, inda aka doke su 6-0.

Chelsea dai ta jefa wa Arsenal kwallaye har hudu a rabin lokaci na farko a wasan wanda shi ne na 1000 da kungiyar ta buga karkashin rikon Arsene Wenger.

''Babu abin da zan ce da kowa da ke wannan kungiyar da kuma masoyanta illa a yi mana afuwa'' Inji Arteta wanda ya kara da cewar ''Mun yi alkawalin za mu yi kokarin gyarawa''.

Arsenal wadda yanzu ita ce ta hudu a teburin gasar ta Premier za ta karbi bakuncin Swansea a ranar Talata.

Karin bayani