Chamberlain da Gibbs ba su yi laifi ba -FA

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Alkalin wasan dai ya nemi afuwa daga bisani.

An wanke 'yan wasan Arsenal guda biyu Alex Chamberlain da Kierian Gibbs daga aikata laifin da ya kai aka kori Gibbs bisa kuskure a wasansu da Chelsea ranar Assabar.

Wani kwamitin da hukumar FA ta kafa ya yanke hukunci cewa alkalin wasan ba korar kawai yayi bisa kuskure ba; shi ma laifin da Chamberlain yayi na taba kwallo da hannu bai cancanci hukunci kora ba.

A yanzu dai babu daya daga cikinsu da za a hana wa buga wasa na gaba.

A bisa dokokin wasan kwallon kafa da hukumar FIFA ta tsara dai za a ba dan wasa katin gargadi idan ya taba kwallo da hannu da gangan, za a kore shi ne kawai idan tabawar da yayi ta hana kwallo shiga raga.

Karin bayani