Marriner zai ci gaba da alkalancin wasa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Marriner dai ya roki afuwa kan kuskuren da yayi.

Alkalin wasan nan da ya kori Kieran Gibbs na Arsenal bisa kuskure zai ci gaba da alkalancin wasa a karshen makonnan duk da kuskuren da yayi.

Andre Marriner zai yi alkalancin wasan da Southampton za ta buga da Newcastle ranar Assabar.

Marriner ya ba da bugun fenariti ga Chelsea yayin wasan da ta buga da Arsenal a Stamford Bridge; bayan da Alex Chamberlain ya taba kwallo da hannu da gangan, amma sai ya kori Kieran gibbs.

Jami'an hukumar da ke kula da ladabtar da alkalan wasa sun ce ya kamata a ba Marriner damar gyara kuskuren nan take a maimakon dakatar da shi.

Karin bayani