Beckham zai gina filin wasa a Miami

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Katafaren filin wasa a Miami

Tsohon kyaftin din Ingila, David Beckham ya sanar da shirin gina katafaren filin wasa mai cin 'yan kallo 25,000 a birnin Miami na Amurka.

Dan shekaru talatin da takwas wanda ya yi ritaya daga kwallo a watan Mayun bana, ya sanar da anniyarsa ta kafa kungiyar kwallon kafa a gasar MLS ta Amurka.

Beckham yace "Idan mutane suka tuna Miami, abinda ke zuwa musu shi ne ruwa, dalilinmu na gina filin wasan kusa da ruwa kenan".

Katafaren filin wasan zai kasance kusa da filin wasan kwallon kwando na Miami Heat.

Ana tunanin cewar daga cikin yarjejeniyar Beckham na koma wa LA Galaxy a shekara ta 2007 shi ne na mallakar kungiyar kwallon kafa a gasar kwallon Amurka.

Karin bayani