Kwallon Kafa: sabuwar gasa a Turai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Za a rika yin gasar a shekaru mara kuma a ranakun wasannin sada zumunta.

A ranar Alhamis ne ake saran amincewa da wata sabuwar gasa ta kwallon kafa tsakanin kasashen Turai me suna League of Nations.

Gasar za ta kasance ta uku ga kasashen Turai bayan gasar Kofin Duniya da ta Kofin Kasashen Turai, kuma za a fara ta ne bayan gasar Kofin Duniya ta 2018.

Ba a dai bayar da cikakken bayani kan yadda gasar za ta kasance ba, amma dai za ta kunshi rukuni-rukuni har hudu.

Kuma za a rika ciyar da kasashe gaba zuwa wani rukuni da kuma dawo da su baya ga wadanda ba su yi kokari ba.

Za a kada kuri'ar amincewa da shirin ne a lokacin taron hukumar kwallon kafa ta Turai me mambobi 54, na shekara-shekara a Kazakhstan.