Za a yi kuri'ar daukar mata a wasan golf

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Akwai alamar cewa shirin daukar mata a kungiyar ta wasan Golf zai karbu

Kungiyar wasan Golf ta Royal and Ancient Golf Club da ke Birtania ta bukaci 'yan kungiyar su 2,500 su kada kuri'ar rushe tsarinta na daukar maza kawai.

Kungiyar wadda aka kafa sama da shekaru 200 ta na barin maza ne kawai su shige ta banda mata.

A watan Satumba ne za a yi kuri'a kan shawarar sauya tsarin, kuma alamu na nuna cewa akwai gagarumin goyon baya ga shawarar.

Shugaban klub din na R&A Peter Dawson ya gayawa BBC cewa, ''muna ganin abu ne me kyau ga wasan mu yi sauyin.

Wasa yana sauyawa, al'umma na sauyawa kuma wasan golf wani bangare ne na al'umma.

Muna ganin lokaci yayi da za a yi wannan sauyi.''

Klub din na R&A shi ne ke shirya gasar Golf ta Birtaniya