Liverpool ta cigaba da mamaya a Premier

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan ita ce nasara ta bakwai a jere da Liverpool ta yi a gasar ta Premier a bana

Liverpool ta ci gaba da mamayar da take yi a gasar Premier bayan ta tsira a hannun Sunderland da ci 2-1.

Steven Gerrad ne ya fara ci wa Liverpool din kwallon farko a minti na 39, sai kuma Sturridge ya biyo baya a minti na 48.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne sai Ki-sung Yueng ya rama kwallo daya da ya ci da ka.

Da wannan nasara Liverpool yanzu ta zama ta biyu a tebur da maki daya tsakaninta da Chelsea me maki 69 a wasanni 31.

A daya wasan na Premier West Ham a gidanta ta ci Hull 2-1, inda West Ham din ta zama ta 11 da maki 34, yayin da Hull take ta 13 da maki 33.