Moyes ya dauki alhakin gazawa

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Muna fatan ba zamu dau lokaci me tsawo ba kafin mu farfado , inji Moyes

Kociyan Manchester United David Moyes ya dauki alhakin rashin kokarin kungiyar bayan rashin nasararta a hannun abokan hamayyarsu Manchester City a gida.

United da ke rike da kofin ita ce ta bakwai a tebur kuma maki 18 ne tsakaninta da ta daya Chelsea, bayan ta yi rashin nasara ta shida a gida a hannun City a bana.

Moyes, ya ce, '' ni na zabi 'yan wasan, na dauki alhakin gazawar kuma a ko da yaushe zan dauka. Abin takaici ne.

Da wannan rashin nasarar a hannun City, United ta sha kashi a gida a gasar lig a bana fiye da yadda ta sha a shekaru uku baya gaba daya.

Moyes ya kara da cewa, ''kowa ya san wannan aiki ne da zai bukaci dan lokaci kafin mu samu yadda muke so,amma kuma yadda aikin yake ke nan.''

Karin bayani