Sevilla ta damawa Real Madrid lissafi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Real Madrid ta salwantar da damammakin da ta samu a kashin farko na wasan

Sevilla ta damawa Real Madrid lissafi bayan da ci ta 2-1 a gasar La Liga ta Spain.

A wasan da suka yi a gidan Sevilla, Real ce ta fara ci ta hannun Cristino a minti 14 da fara wasa.

Minti biyar tsakani sai C. Bacca ya rama, kuma bayn hutun rabin lokaci ya kara ta biyu a minti na 72.

Real Madrid ita ce ta uku a tebur yanzu da maki 70 a wasanni 30.

Atletico Madrid tana ta daya da maki 73, yayin da Barcelona wadda ta ci Celta de Vigo 3-0 tana ta biyu da maki 72.

Karin bayani