Inter Milan na sha'awar Sagna

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Har yanzu Bacary Sagna bai sabunta kwantiraginsa da Arsenal ba

Kungiyar Inter Milan ta Italia na sha'awar daukar dan wasan Arsenal Bacary Sagna idan kwantiraginsa ya kare a lokacin bazara.

Shugaban kungiyar Erick Thohir, wanda ya sanar da haka ya ce, yanzu suna da Nagatomo da Jonathan, idan daya ya ji rauni akwai bukatar wani ya maye gurbin.

Saboda haka, ''muke bukatarsa'', inji shugaban.

Sai dai kuma shugaban ya ce ba sa tattaunawa da dan wasan baya na Manchester United, Patrice Evra, wanda ake rade radin kungiyar na sha'awarsa.

Shi dai Sagna, ya koma Arsenal ne a 2007 kuma ya buga wa kungiyar wasanni 275.

Da aka tambayi shugaban na Inter Milan kan ko suna son sayen Fernando Torres na Chelsea ko Edin Dzeko na Man City, Thohir ya ce, suna bukatar wani a gaba.