Guardiola ya kalubalanci 'yan wasansa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Pep Guardiola ya kai Bayern Munich nasarar Bundesliga da ba kungiyar da ta taba yi

Kocin Bayern Munich Pep Guardiola ya hori 'yan wasan kungiyar da su maimaita nasarar da suka yi a kakar bara, inda suka dauki kofuna uku.

A bara kungiyar ta dauki kofin Bundesliga da na kalubale da kuma na Zakarun Turai.

A daren Talata da ta wuce ne kungiyar ta sake daukar kofin gasar Bundesligan kafin gama gasar da wasanni bakwai.

Da wannan nasara suka zamo zakarun gasar har sau 24.

A tarihin Jamus babu wata kungiya da ta yi nasarar cin gasar lig din ta Bundesliga da sauran wasanni masu yawa haka.

Amma duk da haka kociyan yana son kungiyar ta kara dara sa'a