Rodgers: Man City ce za ta dauki Premier

Image caption Rodgers ya ce, ''ni dai na mayar da hankali akan kungiyata''

Kociyan Liverpool Brendan Rodgers ya ce Manchester City ce ke da babbar damar daukan kofin Premier duk da wuce Cityn da suka yi.

Liverpool ce ta biyu da maki daya a bayan Chelsea, City kuma na ta uku da bambancin maki biyu da kuma bashin wasanninta biyu.

Rodgers ya ce, ''ya rage ga sauran kungiyoyin su yi sakaci a ci su, mu dai za mu cigaba da kokari.''

Kociyan ya ce, '' ba wai ina surutu ba ne kawai. A fili take idan City suka ci wasanninsu za su duki kofi.Lissafin a bayyane yake.''

Rodgers ya kara da cewa, '' mu ne na biyu, ba zan ce ba ma hankoron dukar kofin ba mu ma, idan nace haka na yi karya.''

A ranar 13 ga watan Afrilu ne Liverpool za ta karbi bakuncin City, kuma Chelsea ta zo mata gida ranar 27 ga watan.