Hiddink zai maye gurbin Van Gaal

Hakkin mallakar hoto All Sport
Image caption Guus Hiddink

Tsohon kocin Chelsea, Guus Hiddink zai maye gurbin Louis van Gaal a matsayin kocin Holland bayan kamalla gasar cin kofin duniya a Brazil.

Van Gaal mai shekaru 62 ana tunani zai zama kocin Tottenham a kakar wasa mai zuwa.

Hiddink mai shekaru 67, zai jagoranci kasar har zuwa gasar cin kasashen Turai a 2016 sannan daga bisani Danny Blind ya maye gurbinsa.

Blind da tsohon dan wasan Manchester United Ruud van Nistelrooy za su kasance mataimakan Hiddink.

A baya Van Gaal ya jagoranci Ajax da Barcelona da kuma Bayern Munich.

Karin bayani