Everton ta jefa Fulham cikin hadari

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rabon da Everton ta yi nasara a wasanni biyar a jere a Premier tun farkon lokacin David Moyes a 2002.

Everton ta cigaba da kokarin da take yi a gasar Premier na samun gurbin shiga gasar zakarun Turai, inda kuma ta kara tura Fulham cikin matsala da ci 3-1.

Minti 50 da fara wasa David Stockdale na Fulham ya ci kansu da kansu, kafin Ashkan Dejagah ya rama a minti na 71.

Sai dai kuma a minti na 79 Kevin Mirallas ya kara jefa kwallo ta biyu ragar Fulham,kana kuma a minti na 87 Naismith ya biyo baya da kwallo ta uku.

Everton yanzu tana ta biyar a tebur a bayan Arsenal da bambancin maki hudu.

Yanzu maki biyar ne tsakanin Fulham da faduwa daga Premier, yayin da ya rage mata wasanni shida a gasar.