Liverpool ta hau saman tebur

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Suarez na murnar cin kwallo ta biyu da ya jefa ragar Tottenham a minti na 25

Kungiyar Liverpool ta zama ta daya a Premier bayan ta kunyata Tottenham da ci 4-0.

Minti biyu da fara wasa Younes Kaboul ya ci kansu bayan da Glen Johnson na Liverpool ya kwararo wata kwallo a kasa.

Daga nan ne Liverpool ta kama hanyarta ta nasara sau takwas a jere a gasar ta Premier.

Can a minti na 25 ne kuma sai Luis Suarez ya kara ta biyu bayan dan bayan Tottenham Micheal Dawson ya yi kuskure.

Minti goma da dawowa daga hutun rabin lokaci sai Philippe Coutinho ya kara ta uku daga tazarar yadi 25, kafin Jordan Henderson ya cike ta hudu a minti na 75 da bugun tazara.

Da wannan nasara Liverpool ta shige gaban Chelsea da maki biyu a matsayin ta daya, tana kuma gaban Manchester City ta uku da maki 4, amma City tana da bashin wasanni biyu.

Idan Liverpool ta ci wasanninta shida da suka hada da karonta da Chelsea da Man City a nan gaba za ta dauki Premier karon farko tun kakar 1989-90.

Karin bayani