'Man U za ta iya doke Bayern Munich'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Cin da Robben ya yi wa Man United a Old Trafford shi ya kai Bayern wasan kusa da karshe na kakar 2009-10.

Dan wasan Bayern Munich na gefe Arjen Robben yana ganin Manchester United za ta iya yin galaba a kansu idan Zakarun Turan ba sa kan ganiyarsu ranar Talata.

A ranar Talata ne kungiyoyin za su fafata a wasan dab da na kusa da karshe karon farko a Old Trafford.

Robben ya kara da cewa, ''wasa ne me zafi a don haka sai mun kiyaye.''

dan wasan , ya ce, ''mutane da kafafen yada labarai na ganin Manchester United na cikin matsala a don haka suke gani zamu wuce ne kai tsaye zuwa wasan kusa da karshe, amma ba na son jin haka sam.''

Bayern Munich za ta yi wasan da United da kwarin guiwar cewa wasa daya kawai ta yi rashin nasara a cikin watanni 12, da Man City a matakin rukuni na gasar Zakarun Turai.

Ko da ike dai Bayern ta yi rashin nasara a wasan 3-2, amma kwallon da Robben ya ci ta sa jumulla cin ya zama 4-4.

Hakan kuma ya bai wa kungiyar ta Jamus nasara sabo da bambancin kwallon da ta ci a gidan Man United.