FA ba za ta hukunta Fellaini ba

Hakkin mallakar hoto z
Image caption Dan wasan na Man United ya kafe cewa be aikata laifin ba

Hukumar kwallon kafa ta Ingila FA ba za ta hukunta dan wasan tsakiya na Man United, Marouane Fellaini ba kan zargin tofa wa Zabaleta yawu.

A wani hoto an ga Fellaini yana tsaye gaban dan wasan baya na Manchester City Pablo Zabaleta, a lokacin wasansu na makon da ya wuce.

Dan wasan na fuskantar hukuncin hana shi wasanni uku ne idan da an same shi da laifi.

Wani jami'in hukumar ta FA ya ce, ''bayan da aka duba bidiyon wasan gaba daya ba a ga inda ya aikata laifin ba,''

Fellaini wanda ya yi ta fama da matsaloli tun da ya dawo Man United daga Everton kan fam miliyan 27.5 a watan Satumba da ya wuce har yanzu be ci kwallo ba.

Duk da haka ana sa ran Fellaini me shekara 26 zai yi wasan da United za ta yi da Bayern Munich na Zakarun Turai a Old Trafford ranar Talata.