An kasa aikin filin wasan Man City biyu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A shekarar 2003 ne Manchester City ta koma filin na Etihad

Manchester City ta sanar da kasa aikin fadada filin wasanta gida biyu daga me daukan 'yan kallo 47, 670 zuwa 62,170.

Za a fara aikin ne da fadada benen sashen kudu inda filin zai zama me daukar 'yan kallo 54,000 nan da zuwa farkon kakar wasanni ta 2015-16.

Kuma da zarar an kammla aikin wannan sashen za a koma sanshen arewa shi ma a fadada shi.

Kamfanin da aka ba aikin, Laing O'Rourke shi ne daman ya gina filin domin wasannin Commonwealth na 2002 lokacin yana daukar 'yan kallo 38,000.