Amurka ta dauki tsohon kocin Najeriya

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Amurka na fatan cin amfanin Berti Vogts a gasar Kofin Duniya a Brazil

Amurka ta dauki hayar tsohon kociyan Najeriya Berti Vogts a matsayin me ba da shawara na musamman kan gasar Kofin Duniya.

Vogts dan kasar Jamus ya horad da 'yan wasan Najeriya, Super Eagles sama da shekara daya kawai.

Amma ya ajiye aiki bayan rashin tabuka abin a-zo-a-gani a gasar Kofin Kasashen Afrika ta 2008.

Amurka na rukuni daya da Ghana a gasar cin Kofin Duniya da za a yi a Brazil.