Manchester United ta rike Bayern Munich

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Manchester United na da kwarin guiwa a karo na biyu kan yadda ta yi wasa

Manchester United ta tashi da Bayern Munich 1-1 a karonsu na farko na wasan dab da na kusa da karshe na Zakarun Turai.

Nemanja Vidic ne ya sa Man United a gaba minti 58 da wasa da kwallon da ya ci da kai.

Sai dai kuma minti takwas tsakani sai Schweinsteiger wanda aka kora daga bisani ya ramawa Bayern.

Bayern Munich na da dama fiye da Man United saboda kwallon da ta sa a Old Trafford.

Amma ana ganin wasan da aka yi a Old Trafford ya sa Man United din na da fatan rikita lissafin Zakarun na Turai da Jamus idan suka hadu ranar Laraba me zuwa.

Schweinsteiger wanda aka kora saboda ketar da ya yi wa Rooney bayan an bashi katin gargadi da farko ba zai yi wasa na biyun ba.

A ranar Laraban nan ne kuma za a ci gaba da wasanin na Zakarun Turai, tsakanin Real Madrid da Borussia Dortmund da kuma PSG da Chelsea.

Karin bayani